17 Mayu 2021 - 13:01
Fadar Shugaban Kasar Chadi Ta Karbi Bakuncin Ministan Harkokin Wajen Kasar Qatar

Shugaban Majalisar rikon kwarya na kasar Chadi, Janar Muhammad Idriss Deby ya karbi bakuncin ministan harkokin wajen kasar Qatar a jiya Lahadi.

ABNA24 : Ministan harkokin wajen na kasar Qatar ya tabbatar da cewa;kasarsa tana bayar da cikakken goyon baya ga gwamnatin rikon kwarya ta soja, kamar kuma yadda take son ganin an ci gaba da samun hadin kai a kasar.

Har ila yau, babban jami’in diplomasiyyar na kasar Qatar ya kuma jinjinawa kasar Chadi saboda yadda take taka rawa wajen fada da ta’addanci.

Har ila yau kasashen biyu sun tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakaninsu, tare da yin ishara da kafa alakar diplomasiyya a tsakaninsu tun 1984.

342/