ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press na kasar Iran ya bayyana cewa taron ya hada ministan man fetur na kasar Iran Bijan Zangeneh da ministan wutan lantarki na kasar Iraki Majid Mahdi Hantoush da wasu jami’an gwamnatin kasashen biyu a nan Tehran inda suka tattauna wannan batun.
Ministan man fetur na kasar Iran ya fadawa Iran Press kan kan cewa ya zuwa yanzu iran ta sayarwa Iraki iskar gas cubic mitre billiyon 27 na iskar gas amma akwai matsalar ta yadda za’a biya kudaden. Amma ya ce ya na fatan tare da wannan ziyarar da Majid Mahdi da tawagarsa suka kawo nan Tehran za’a warware batun.
A cikin ‘yan watannin da suka gabata ne kamfanin iskar gas na kasar Iran ya rage yawan iskar gas da yake turawa kasar ta Iraki saboda taruwar basussuka.
342/