ABNA24 : Gidanen kurkukun kasar ta Zimbabwe an gina su ne domin su dauki mutane 17,000,amma an cunkusa mutane 22,000 a cikinsu. Shugaban kasar ta Zimbabwe Emmersson Mnangagwa ne ya sanar da yi wa fursunonin afuwa. Fursunonin da afuwar ta shugaban kasa ta shafa, sun kunshi wadanda ba su aikata manyan laifuka ba.
Daga cikin matakan da ake dauka na hana yaduwar cutar a gidajen kurkuku da akwai hana kai ziyara sannan kuma da yi wa fursunoni allurer rigakafi. Ya zuwa yanzu dai adadin wadanda su ka kamu da cutar corona a kasar Zimbabwe sun kai 37,534, wadanda kuma su ka mutum sun kai 1,551, kamar yaadda hukumar da ke sa ido akan cutuka masu yaduwa ta kasar ta bayyana.
342/