ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Imam Khamina’i ya na fadar haka a wata wasika da ya aikewa babban kwamandan dakarun na IRGC, Manjo Janar Husain Salami a safiayar yau Laraba, ranar da aka ware a matsayin ranar dakarun na IRGC, wanda kuma ya yi dai dai da ranar haihuwar limami na 3 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Allah (s) wato Imam Husain dan Ali (a).
An kafa dakarun IRGC nr, jim kadan bayan nasarar Juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran, wanda Imam Khomaini(q) ya jagoranta zuwa nasara a shekara 1979, da nufin tabbatar da tsaro a ciki da wajen kasar. IRGC dai sun taimaka a yaki tsakanin Iran da Iraki daga 1980-1988.
Sannan sun sami nasarori da dama a fagen samar da kayakin yaki da kuma kare kasar daga makiya. A bangaren kasashen waje kuma, dakarun na IRGC sun taimaka wajen wargaza kungiyar Daesh wacce Amurka ta samar a kasashen Iraki da Syriya a shekara ta 2014.
Da wannan dalilin ne Amurka ta sanya dakarun na IRGC cikin kungiyoyin yan ta’adda a wajenta, sannan shugaban kasar Amurka da ya shude, Donal Trump ya bada umurnin kashe kwamandan rundunar Qudus ta dakarun wato Janar Qasim Sulaimani a ranar 3 ga watan Janerun shekara ta 2020.
342/