1 Maris 2021 - 07:18
​Imam Khamenei: Kasashen Turai Ba Su Da Gaskiya A Tattaunawarsu Da Iran Kan Shirinta Na Nukiliya

Jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Iran ya bayyana cewa, kasashen turai ba su da gaskiya a tattaunawarsu da Iran kan shirinta na nukiliya.

ABNA24 : A cikin wani bayaninsa da aka saka a shafinsa na twitter, Jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Iran ya bayyana cewa, a tattaunawarsu da Iran kan shirinta na nukiliya, kasashen turai ba su nuna gaskiya ba, maimakon haka ma sai karairayi da suke ta yi da nufin yaudarar kasar ta Iran.

Ya ce Iran tana sane da abin da suke nufi, kuma ta shiga tattaunawar ne domin yanke uzuri a kansu, amma ba wai domin ta dogara da su ba ne.

Ya ci gaba da cewa, suna hankoron ganin sun raunana Iran ne ko ta wace hanya, tare da hana ta mallakar hatta makaman da za ta iya kare kanta daga barazanar makiya, wanda kuma hakan ba abu ne da mai hankali zai aminta da shi ba.

Ya jaddada cewa Iran tana nan kan bakanta na ci gaba da aiwatar da shirinta na nukiliya na zaman lafiya, kuma za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace a kan shirinta a duk lokacin da ta ga ya dace.

342/