ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran kasar Italiya AKI ya bayar da rahoton cewa, a yammacin jiya Juma’a, ministan harkokin wajen kasar Luigi Di Maio ya fitar da sanarwar cewa, daga yanzu sun dakatar da sayar wa kasar Saudiyya da makamai har sai abin da hali ya yi.
Ministan harkokin wajen kasar ta Italiya ya ce, sun dauki wannan matakin ne bisa la’akari da cewa, ana yin amfani da wadannan makaman ne wajen kisan fararen hula a kasar Yemen, wanda hakan ya saba wa ‘yan adamtaka, a kan haka sun dakatar da duk wata mu’mala ta cinikin makamai da gwamnatin Saudiyya.
Ya ci gaba da cewa, wanann matakin ba zai takaitu da kasar ta Saudiyya ba kawai, zai shafi har da kasar hadaddiyar larabawa UAE, wadda ita ma tana daga cikin kasashen da suke kaddamar da wannan yaki a kan al’ummar kasar Yemen, wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyyar kashe dubban fararen hula mata da kananan yara, tare da rusa kasar, da kuma jefa al’ummarta cikin matsanancin hali na rayuwa.
342/