24 Janairu 2021 - 15:44
Iraki:Akalla Mayakan Hashadushabi 11 Ne Kungiyar Daesh Ta Kashe A Arewacin Bangadaza

Wata majiyar jami’am tsaro a kasar Iraki ta bayyana cewa mayakan dakarun Hashadu Alsshabi 11 mayakan Daesh suka kashe a wani harin da suka kaimasu a arewacin birnin Bagdaza a jiya Asabar.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tenhran majiyar tana cewa, mayakan na Daesh sun kaiwa runduna ta 22 ta Hashadu Alshabi ne garin Tikrit babban birnin Lardin salahuddeen a jiya Asabar a cikin duhu.

Wannan harin yana zuwa ne kwanaki biyu kacal da hare-haren kunan bakin wake suka kashe mutane 32 a wata kasuwa a cikin birnin Bagdaza.

Wani daga cikin dakarun Hashdu mai suna Abu Ali al-Maliki ya fadawa kamfanin dillancin labaran AFP kan cewa

Babu wanda ya dauki nauyin harin na Tikrit amma gwamnatin kasar tana tuhumar mayakan Daesh ta kai harin.

342/