13 Disamba 2020 - 10:45
Kasar Masar Ta Karbi Jirgin Farko Dauke Da Allurar Rigakafin Cutar Covid-19

Ministar lafiya Ta kasar Masar Hala Zayed da sauran jami’an Diplomaiysar kasar China da na hadaddiyar daular larabawa ne suka isa filin hauwa da saukar jiragen saman na birnin Alkahira domin tarbar jirgin farko dake dauke da Allurar rigakafin kamuwa da cutar korona Virus da kasar China ta samar.

ABNA24 : An yi gwajin Allurar a Hadaddiyar Daular Larabawa kuma sun bayyana cewa tana da tasiri sosai fiye da kashi 86 cikin dari.

Cutar koron ta kara kamari a yan makwannin nan a kasar Masar, kasar larabawa da ta fi yawan jama’a a duniya lamarin ya da ya janwo gwamnati ta yi gargadin sake rufe kasar a karo na biyu idan cutar ta ci gaba da yaduwa kamar wutar daji.

Gwamnatin Masar ta sanar cewa tana so ta fara yin Allurar Rigakafin ne kan ma’aikatan lafiya, musamman wadanda suke kula da masu dauke da cutar Korona,

Allurar rigakafi ta Sinopharm an amince a yi amfani da ita ne a wasu kasashen a yanayi na gaggawa, kuma har yanzu ana ci gaba da gwajin maganin a wasu kasahe 10, kuma magani yana kashe kwayoyin cuta ne kamar yadda Allurar rigakafin Polio ke aiki.

342/