ABNA24 : Hatami ya bayyana haka ne a jiya Lahadi a lokacinda yake tattaunawa da wata tashar talabijin ta cikin gida dangane da dage takunkuman saya da seyar da makamai kan kasar a jiya Lahadi.
Ministan ya kara da cewa wasu kasashen duniya musamman Amurka su na tsammanin cewa ba wata kasa da za ta ci gaba a duniya ba tare da taimakonsu ba. Takunkuman da aka dorawa kasar Iran sun taimakawa kasar wajen samun wadata daga sayan makamai da wasu kayakin soje daga kasashen waje.
Hatami ya ce babu shakka a bangaren samar da jiragen yaki da na leken asiri wadanda ake sarrafasu daga nesa kasar Iran ta na daga cikin kasashen 6 a duniya masu fasahar kerasu.Har’ila yau dangane da makamai masu linzami kuma Burgediya Janar Hatami ya ce kasar Iran ta ci gaba sosai a wannan bangaren.
Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta yi kokarin ganin an tsawaita takunkuman. Da ta kasa, sai ta fara shirin ganin an dorawa kasar sabbin takunkumai, ta yadda ko an dage wannan an sake dora mata sabo , amma kwamitin tsaro na MDD ta ki amincewa da hakan.
342/