ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Saumaria ya bayar da rahoton cewa, a jiya wasu wadanda ba a san ko su wane na ba sun saka wuta wadda ta jawo gobara a cikin asibitocin tafi da gidanka guda biyu na rundunar sa kai ta al’ummar Iraki Hashd Sha’abi, a birnin Najaf da ke kudancin kasar.
Rahoon ya ce, rundunar sa kai ta al’ummar Iraki Hashd Sha’abi ta kafa wadannan asibitocin ne domin bayar da taimakon gaggawa ga jama’a masu ziyarar arba’in.
An kunna wutar ne da gangan, kuma hakan ya yi sanadiyyar konewar dukkanin kayan aiki da ke cikin wadannan asibitoci, da kuma tarin magunguna da aka tanada domin hidima ga jama’a.
Jami’an tsaro dai sun shiga gudanar da bincike kan faruwar lamarin, da zimmar ganin an kame duk wadanda suke da hannu a cikin lamarin.
Dakarun Hashd Sha’abi dai su ne suka taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen ‘yan ta’addan daesh a Iraki, tare da yin aiki kafada da kafada tare da jami’an tsaron Iraki wajen tabbatar da tsaro a fadin kasar.
Gwamnatin Amurka tana tsananin nuna adawa da kafa wannan runduna, sakamakon yadda ta kawar da ‘yan ta’adda wadanda suka shigo kasar da sunan kafa abin suke kira daular musulunci, tare da taimakon wasu sarakunan larabawa.
342/