11 Oktoba 2020 - 13:22
Mutum Daya Ya Rasa Ransa A Zanga-zangar Kin Jinin Rundunar “Ya Sanda Ta “SARS” A Nigeria

Masu Zanga-zangar a garin Ogbomosho da ke jahar Oyo, suna nuna kin jininsu ne da rundunar nan ta ‘ya sanda mai fada da ‘yan fashi da makami wacce ake kira da “ SARS’, a lokacin da jami’an ‘yan sanda su ka hareb daya daga cikinsu.

ABNA24 : Wani rahoton na jaridar Sahara Reporters ya ambaci cewa; harsashin ‘yan sandan ya sami wasu Karin masu Zanga-zanagr biyu.

Mutumin da ya rasa ransa, dalibi ne, yayin da wani kuma yake kwance rai kwakwai, mutum kwakwai.

A jahar Delta da kuma birnin tarayyar Abuja, masu Zanga-zangar kamar rundunar ‘yan sanda ta SARS’ sun gamu da fushin jami’an tsaro duk da cewa an gudanar da Zanga-zangar ne a cikin ruwan sanyi.

Ana zargi wannan rundunar ne dai da cin zarafin ‘yan kasa da ya hada da wulakanta su da kuma kisa a wasu lokutan.

A makon da ya shude ma dai mataimakin shugaban kasar ta Nigeria Osinbanjo ya soki lamirin runudunar saboda kashe wani saurayi da ta yi, tare da fadin cewa; An wayi gari al’ummar Nigeria ba su iya tantance tsakanin ‘yan sanda da kuma ‘yan fashi.

342/