10 Oktoba 2020 - 12:41
Buhari Ya Bukaci A Kwantar Da Hankali, Ya Bukaci Hukumar ‘Yan Sanda Da Ta Yi Gyara Kan Rundunar SARS

Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya kirayi al’ummar kasar da su kwantar da hankalinsu dangane da damuwar da suke da ita kan rundunar SARS da ke yaki da ‘yan fashi da makami kamar yadda kuma ya bukaci sufeto janar na ‘yan sandan Nijeriyan da ya dau matakan da suka dace wajen yin kwaskwarima wa rundunar da kuma kawar da damuwar da mutane suke da ita kan rundunar.

ABNA24 : Shugaba Buharin ya ba da wannan umurni a daidai lokacin da ake ci gaba da samun zanga-zangogin nuna rashin amincewa da ayyukan cin zarafin al’umma da wasu ‘yan sanda na rundunar ta SARS suke yi a bangarori daban-daban na kasar inda suke kiran da a rusa rundunar kwata-kwata.

Shugaban na Nijeriya ya ce tuni ya ba wa Sufeto Janar na ‘yan sandan Muhammad Adamu umurnin ya magance wannan damuwa da mutane suke da ita kan rundunar ta SARS da kuma hukunta duk wadanda aka same su da laifin take hakkoki da cin zarafin al’umma. Har ila yau shugaban ya ce yana kiran masu al’umma da su kwantar da hankulansu, duk kuwa da cewa suna da hakkin bayyanar da ra’ayinsu.

Ita dai wannan runduna ta SARS an kafa ta ne da nufin fada da fashi da makami da sauran manyan laifuffuka, to sai a baya-bayan nan al’umma suna korafi kan yadda suke cin zarafin al’ummar da ba su ci ba su sha ba lamarin da ya sanya karuwar kiraye-kirayen da aka rusa rundunar.

342/