15 Satumba 2020 - 12:11
​Iran Ta Musanta Zargin Amurka Dangane Da Labarin Jaridar Politico

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta musanta zargin gwamnatin Amurka kan kasar don neman kuri’a a zaben watan Nuwamba na karshen wannan shekara.

ABNA24 : Bayanin ya ce gwamnatin kasar Iran tana kiyaye dokokin diblomasiyya a dukkan ayyukanta, amma sabanin gwamnatin Amurka.

Bayanin ya kammala da cewa hatta kissan Shaheed Qaseem Sulaimani gwamnatin kasar Iran zata bi hakkinta kan jami’an gwamnatin Amurka wadanda suke da hunnu a cikin kissan ta hanyar dokokin kasa da kasa.

Kafin haka dai Jaridar POLITICO ta kasar Amurka ta buga labarin cewa gwamnatin kasar Iran tana son kashe jakadan Amurka a Afrika ta kudu, dalilin da ta bayan kenan wajen kissan Janar Qasim Sulaimani a farkon wannan shekara a kasar Iraki.

342/