13 Satumba 2020 - 11:57
An Koma Aikin Gwajin Allurar Rigakafin Cutar Korona

Kamfanin sarrafa magunguna na AstraZenaca da kuma jami’ar Oxford, sun sanar da komawa akan aikin gwajin allurar rigakahin cutar korona, bayan dakatar da shi.

ABNA24 : A ranar Talata data gabata ce bangarorin suka sanar da dakatar da gwajin ne, bayan da daya daga cikin mutanen da ake amfani da maganin a kansu a Biritaniya ya kamu da wata rashin lafiya da ba’a fahimce ta ba.

Saidai a jiya Asabar, jami’ar Oxford ta bayyana cewa za’a ci gaba da gwajin wanda ta ce yana da tabbaci.

Maganin dai ana bayyana shi a matsayin mai inganci tsakanin gomman alluran da ake kan gwaji kansu yanzu haka.

Dama dai jami’ar ta ce akwai yiwuwar wasu daga cikin wadanda ake gwajin kansu su fusnkanci wasu larurori.

342/