ABNA24 : Palasdinawan da ke gabashin garin Ramallah sun ne kare kansu daga harin ta’addanci na yahudawa ‘yan share wuri zauna, inda su ka jikkata uku daga cikinsu.
Majiyar Palasdinawan ta ambaci cewa; Samarin palasdianwa a garin Dei-Jarir ne su ka yi taho mu gaba da ‘yan sahayoniya da suka kai musu hari tare da goyon bayan sojojin.
Sojojin na ‘yan sahayoniya sun ja daga a kusa da rukunin gidajen ‘yan share wuri zauna na Kuhaf Hashajir domin bayar da kariya da goyon baya ga yahudawan.
A gefe daya, kakakin kungiyar Hamas, Hazim Kassim ya bayyana cewa; kamen da sojojin sahayoniya suke yi wa Palasdinawa a yammacin kogin Jordan da suka hada da ‘yan majalisar dokokin palasdinu, wani yunkuri ne babu inda zai kai su.
342/