ABNA24 : Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, jirgin na Iran ya isa ne dauke da kayayyakin bukatar gagagwa na ayyukan likita, da kuma wasu kayan da ake bukata domin taimaka ma jama’a cikin gaggawa, musamman ma wadanda abin ya shafa.
A jiya shugaba Rauhani ya sanar da shugaban kasar Lebanon cewa za ta aike da kayan taimakon gaggawa zuwa kasar ta Lebanon, wanda jirgi na farko ya fara kama hanya a daren jiya, kuma ya isa Beirut da jijjifin safiyar yau.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Iran ta sanar da cewa, akwai wasu jiragen da suke shirin kama hanya zuwa Beirut dauke da wasu kayayyakin.
Ministan lafiya na kasar Lebanon ya sanar a safiyar yau Alhamis cewa, adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamkon abin da faru, ya kai 137, yayin da wasu dubbai suke ci gaba da karbar magani a asibiti.
342/