4 Agusta 2020 - 12:15
Usman Kaba Ya Shelanta Kansa A Matsayin Dan Takarar Shugaban kasar Guine A Bangaren ‘Yan Hamayya

A ranar Asabar da ta gabata ne dai Usman Kaba ya zama na farko wanda aka bayyana a matsayin dan takarar shugabancin kasar a banagren ‘yan hamayya a kasar ta Guinea.

ABNA: An tsayar da watan Oktoba a matsayin lokacin da za a gudanar da manyan zabuka a kasar ta Guinea.

Jam’iyyar da ta tsayar da Usman takara “ Party Of Democrats for Hope” wacce a takaice ake kira ( Pades) an kafa ta ne a 2017.

Shi dai Usman Kaba ya yi aiki tare da shugaban kasar ta Guinea na yanzu Alpha Conde wanda aka zabe shi ta tafarkin demokradiyya a karon farko a kasar a 2010.

A shekarun baya dai kasar ta Guinea ta fuskanci tashe-tashen hankula na siyasa. A Jiya Lahadi ma an yi taho mu gama a tsakanin ‘yan hamayya da magoya bayan jam’iyya mai mulki da hakan ya yi sanadin mutuwar mutane 10.

‘Yan hamayyar siyasar kasar ta guinea suna zargin cewa shugaban kasar Conde dan shekaru 82 yana shirya makarkashiyar sauya tsarin mulki domin yin tazarce.

342/