ABNA24: Sai a watan Nuwamba mai zuwa ne kotun tsarin mulkin kasar zata sanar da matsayinta kan takarar ta shugaba Museveni.
Idan ya sake tsayawa takara ya kuma lashe zaben, M. Museveni dake shugabancin kasar na tsawon shekaru 34, zai sake yin wani wa’adin mulki na shekara biyar nan gaba.
Duk da cewa har yanzu jam’iyyun hamayya basu tsayar da dan takara ba a zaben na watan Janairun badi, wanda ake ganin shi ne babban abokin hammayar shugaba Museveni shi ne mawakin nan kuma dan siyasa Robert Kyagulanyi, wanda akafi sani da sunan Bobi Wine, wanda kuma ke da farin jinin sabbin masu kada kuri’a.
A cikin shekara 2017 ne jam’iyya mai mulki a kasar ta Uganda, ta yi amfani da rinjayen da take da shi a majalisar dokokin kasar domin amincewa da kudirin kayyade shakarun tsayawa zaben shugabancin kasar, wanda kuma ‘yan adawan kasar ke ganin tamakar an share wa M. Museveni hanyar ci gaba da shugabancin kasar har tsawon rayuwarsa.
342/