(ABNA24.com) Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta bayyana cewa an kammala taron na yau ne tare da rattaba hannu kan yarjejeniyar tallafawa juna kan al-amuran tsaro tsakanin kasashen biyu.
Bayan taron ne dai Ali Ayyub ministan tsaron kasar Siriya ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ta kasa durkusar da kasashen Iran da Siriya da kuma kasashen masu gwagwarmaya a yankin saboda hadin kai da taimakon juna da ke tsakaninsu.
Ayyub ya kara da cewa duk abinda gungun kasashe masu gwagwarmaya suka cimma suna dabbakaci a aikace, duk tare da yawan asarar rayuka da dukiyoyi da zake yi, don hakan ya fi mika kai ga bukatun makiya. Daga karshe ministan ya bayyana cewa gwamnatin kasar Siriya za ta sami nasara a duk fagagen da take yaki da makiya saboda jajircewar sojoji da mutanen kasar kan zama ‘yantattun mutane.
342/