15 Yuni 2020 - 07:52
 Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Nuna Banbancin Launin Fata A Kasar Amurka

A jiya Lahadi ma an gudanar da Zanga-zanga a cikin birane da dama na kasar ta Amurka da su ka hada da New York, Washington, Atlanta da Philadelphia.

(ABNA24.com) A jiya Lahadi ma an gudanar da Zanga-zanga a cikin birane da dama na kasar ta Amurka da su ka hada da New York, Washington, Atlanta da Philadelphia.

Masu Zanga-zangar a cikin mafi yawancin biranen na Amurka sun daga kwalaye da su ke dauke da taken cewa; Rayuwar Bakaken Fata Tana Da Muhimmanci”

A birnin New York ma an gudanar da gangami a kusa da fadar White House.

Amurka ta tsunduma cikin matsala tun bayan kashe Goerge Floyd da ‘yan sanda su ka yi a garin Minneapolis kusan makwanni uku da su ka gabata.



/129