6 Yuni 2020 - 05:43
Brazil : Bolsonaro, Ya Yi Barazanar Janye Kasarsa Daga WHO

Shugaban kasar Brazil, Jair Bolsonaro, ya ce zai bi sahun Amurka, wajen janye kasarsa daga hukumar lafiya ta duniya, WHO, saboda zarginta da nuna bangaranci a cikin aikinta.

(ABNA24.com) Shugaban kasar Brazil, Jair Bolsonaro, ya ce zai bi sahun Amurka, wajen janye kasarsa daga hukumar lafiya ta duniya, WHO, saboda zarginta da nuna bangaranci a cikin aikinta.

Da yake sanar da hakan ga manema labarai, M. Bolsonaro, ya ce, ina mai shaida muku cewa, Amurka ta fice daga WHO, mu ma muna tunanin yin hakan nan gaba, muddin hukumar, ba ta canza ba.

Furincin na Bolsonaro, na zuwa ne kwana guda bayan da kasar ta zama ta uku wajen yawan mutanen da annobar korona ta kashe a duniya, inda ta ke da mutum sama da 34,000.

Wasu dai na alakanta ta’adin da annobar ta yi a Brazil, kan kin amincewa da matakan kulle da shugaban kasar ya yi, wanda a cewarsa zai jefa kasar cikin wani bala’I mafi muni fiye da annobar ta korona.



/129