13 Mayu 2020 - 06:20
Iran: An Gabatar Da Doka Mai Kalubalantar Isra'ila A Majalisar Dokoki

Majalisar dokokin kasar Iran ta gabatar da wata doka ta bayyana matsayin JMI dangane da ta’asan da HKI take aikatawa a kasar Palasdinu, da kuma yankin gabas ta tsakiya.

(ABNA24.com) Majalisar dokokin kasar Iran ta gabatar da wata doka ta bayyana matsayin JMI dangane da ta’asan da HKI take aikatawa a kasar Palasdinu, da kuma yankin gabas ta tsakiya.

Tashar talabijin ta Alalam a nan Tehran ta nakalto shugaban kwamitin harkokin waje na Majalisar, Mujtaba Zannoor yana fadar haka a safiyar yau Talata.

Zannoor ya kara da cewa a mako mai zuwa ne ake saran majalisar zata kammala aikin kafa dokar mai maadoji 14. Labarin ya kara da cewa majalisar ta bukaci a gaggauta kafa dokar don muhimmancinta da kuma nunawa yahudawan matsayin JMI a kan barazanar da take yiwa kasashen yankin da Falasdinu.

Dokar dai bukaci gwamnatin JMI ta amince da kasar Falasdinu a matsayin kasa ta asalin falasdinawa mazauna kasar, wadanda suka hada da musulminsu, kiristoci da yahudawa, ba ta wadanda suka zo daga ba ya ba.

Har’ila yau ta bukaci gwamnatin JMI ta amince da birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar Falasdinu ta har abada, sannan ma’aikatar harkokin wajen kasar ta kammala shirin bude ofishin jakadanci ko kuma karamar ofishin jakadanci na Iran a birnin Qudus ta yanar gizo.

Daga karshe dokar ta bukaci ma’aikatar shari’ar kasar ta dauki duk wata yayi mu’amala da HKI a matsayin aikata fasadi a bayan kasa kuma hukuncinsa shi ne mafi tsananin ukuba .


/129