(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, babu bukatar gudanar da wata tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan batun musayar fursunoni.
Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabtar da wani jawabi a jiya a gaban kwamitin kula da siyasar waje a majalisar dokokin Iran, ministan harkokin wajen kasar Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa; musayar fursunoni ba batu ne da ke bukatar gudanar da wata tattaunawa tsakanin Amurka da Iran ba.
Zarif ya ce, jami’an da suke kula da harkokin kasashen biyu a cikin kasashensu za su iya aiwatar da wannan shiri, ba tare da wata ganawa ta kai tsaye tsakanin jami’an gwamnatocin Iran da Amurka ba.
Jakadan kasar Switzerland dai shi ne ke kula da lamurra da suka shafi Amurka a Iran, kamar yadda jakadan Pakistan a Washington shi ne ke kula da lamurra na Iran a kasar Amurka
Akwai Iraniyawa da Amurka take tsare da su a cikin kasarta wadanda take zarginsu da alaka da wasu bangarori na gwamnatin Iran, kamar yadda ita ma Iran tana tsare da wasu Amurkawan bisa tuhumce-tuhumce daban-daban, daga ciki har da leken asiri, da kuma shigowa cikin kasarta ba bisa ka’ida ba.
/129
12 Mayu 2020 - 07:57
Lambar labari: 1036019
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, babu bukatar gudanar da wata tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan batun musayar fursunoni.