20 Afirilu 2020 - 06:32
Mutum Sama Da 160,000 Cutar Corona Ta Kashe A Duniya

Alkalumman baya bayan nan da kamfanin dilancin labaren AFP, sun nuna cewa mutum dubu 160 da 685 ne cutar coronavirus, ta yi ajalinsu a fadin duniya tun bayan bullarta a watan Disamba bara a kasar China.

(ABNA24.com)  Alkalumman baya bayan nan da kamfanin dilancin labaren AFP, sun nuna cewa mutum dubu 160 da 685 ne cutar coronavirus, ta yi ajalinsu a fadin duniya tun bayan bullarta a watan Disamba bara a kasar China.

Baya ga haka, mutane sama da miliyan 2,334,130 ne suka kamu da cutar a kasashe 193 na duniya.

Adadin mutanen da suka warke daga cutar sun kai 518,900 a cewar alkalumman, ke kamfanin AFP ke fitarwa wadanda suka dogara daga abunda hukumomin kasashen da hukumar WHO ke sanarwa.

Amurka wacce ta fara samun mutun na farko da yam utu sanadin cutar a watan Fabrairu, ita ce a yanzu kasar data fi yawan masu fama da cutar da mamata inda ta ke da 39,090 da suka mutu daga cikin 735,287 da suka kamu.

Sauren kasashen bayan Amurka, sun kasance ne a nahiyar turai, wadanda suka hada da Italia, Spain, Faransa, da kuma Biritaniya.


/129