8 Afirilu 2020 - 06:47
Rundunar Sa Kai Ta “Hashd al-Sha'abi” A Kasar Iraqi Ta Yi Alkawalin Kawo Karshen Mamayar Da Amurka Ta Yi Wa Kasarsu

Rundunar sa-kan ta “Hashd al-Sha'abi” ta bayyana sojojin Amurka da suke cikin kasarsu a matsayin ‘yan mamaya, tare da shan alwashin kawo karshen mamayar tasu

(ABNA24.com) Rundunar sa-kan ta “Hashd al-Sha'abi” ta bayyana sojojin Amurka da suke cikin kasarsu a matsayin ‘yan mamaya, tare da shan alwashin kawo karshen mamayar tasu

A wani bayani da rundunar ta fitar ta ce; Daga yanzu, sojojin Amurka da ke cikin kasar za a rika mu’amala da su a matsayin ‘yan mamaya.

Wani sashe na sanarwar da yake magana da sojojin Amurkan ya ce; “Kun tabbatar da cewa ku sojojin mamaye ne, kuma babu wani harshe da ku ke fahimta in ba na amfani da karfi ba akanku ba. Don haka, za a yi mu’amala da ku ne a bisa wannan ka’ida.”

Har ila yau, wani sashe na bayanin ya ja kunnen Amurkawan da cewa ya zuwa yanzu mayar da martanin da aka yi musu, somin tabi ne kawai akan wuce gona da irin da ku ke yi.


/129