(ABNA24.com) Har ila yau dakarun sun watsa bayanai game da daya daga cikin yan leken asirin da aka kama dan shekaru 60 da haihuwa wanda ke yi wa HKI aikin leken asiri tun daga shekara ta 1994, mutumin ya amsa zargin da ake masa na yi wa HKI aikin leken asiri da kuma ya tona asirin sunayen jami’an tsaron Israila da yake aikawa da bayanan sirri.
Daga cikin ayyukan na sa kamar yadda ya bayyana akwai tattara bayanai da suka shafi manyan kwamandojojin gwagwarmayar palasdinu da kuma jamai’an tsaro, da kuma labaran da suke da alaka da zanga – zangar neman dawowar yan gudun hijira gida ga hukumar lekan asirin Isra'ila.
342