(ABNA24.com) Hujjatul Islam Ra’isi ya bayyana haka ne a jiya Talata a lokacinda aka gudanar da zama ta musamman don ganin irin aikin da louyoyin da aka bawa aikin tattara bayanai da shaidu kan kisan Qasim Sulaimani a nan Tehran.
Ra’isi ya kara da cewa dole ne lauyoyin su tattara dukkan bayanai da shaidu na bayyane da kuma na boye dangane da kissan shahid Sulaimani don tabbatarwa duniya munin shuwagabannin Amurka, a yadda suke mu’amala da sauran kasashen duniya.
A ranar 3 ga watan Jenerun da ya gabata ne Shugaban kasar Amurka mai ci Donal Trump ya bada umurnin a kashe Janar Qasim Sulaimani kwamandan rundunar Qudus ta dakarun juyin juya halin musulunci a birnin Bagdaza na kasar Iraqi. Janar Sulaimani ya je kasar Iraqi ne bisa gayyatar gwamnatin kasar.
Tare da shi, akwai Abu Mahdi al-muhandis mataimakin shugaban dakarun hashdushaabi na kasar ta Iraqi wadanda aka kashesu tare. Har’ila yau akwai wasu mutane 8 tare da su duk sun yi shahada tare da su a lokacinda makamai masu linzami na sojojin Amurka suka tarwatsa motocin da suke ciki a birnin Bagdaza.
/129
12 Maris 2020 - 05:03
Lambar labari: 1016751
Hujjatul Islam Ibrahim Ra’isi alkalin alkaln kasar Iran ya bayyana cewa shari’ar kissan shahid Qasim Sulaimani , shari’a ce wacce take da matukan muhimmanci ga makomar kasar Iran, sannan tana da muhimmanci wajen kunyata azzaluman kasashen duniya a gaban sauran kasashen duniya.