(ABNA24.com) Atoni Janar din jihar Kaduna Aisha Dikko ta bayyana cewa gwamnatin jihar za ta kalubalanci hukuncin Kotu a Kaduna da ta saki mabiya mazhabar shi’a 91.
Rahotanni sun ce Aisha Dikko ta ce dalilan da maishari’a Hajaratu Gwadah ta bada na sakin wadanda ke tsaren bai gamsar da su ba.
A ranar Juma’a ne kotu a Kaduna karkashin maishari’a Hajaratu Gwadah ta yanke hukuncin sakin mabiya mazhabar shi'a 91 da ke tsare tun a shekarar 2015.
Hajaratu ta ce hujjojin da gwamnatin Kaduna ta mika gaban kotu basu yi tasiri ba, a dalilin haka ta yi watsi da da su sannan ta umarci da aka sake su da gaggawa.
Sai dai awowi kadan bayan yanke wannan hukunci, gwamnatin Kaduna karkashin gwamnan jihar Nasiru El-Rufa’i, ta bayyana cewa lallai ba za ta amince da wannan hukunci ba, za ta garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.
A doguwar takarda da Kwamishinan shari’a ta jihar Aisha Dikko ta raba wa manema labarai, ta ce hujjojin da suka mika masu karfi ne kwarai sai dai idan kotun ba su bisu dalla-dalla ba.
/129