Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta ba da labarin lalata wata radar gargaɗi na farko mallakar sojojin Amurka a Bahrain kuma ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne a matsayin martani ga harin sama da Amurka ta kai wanda ya shafi wata hasumiyar sadarwa a yankin Sirik.
Ofishin Hulɗar jama'a ta sojin ruwa na Rundunar Kare Juyin Juya Hali ta bayyana cewa mayaƙan rundunar sararin samaniya ta Rundunar, sa'o'i kaɗan da suka wuce, sun kai hari kuma sun lalata wata radar gargaɗin farko mallakar sojojin Amurka a tsibirin Bahrain. An ɗauki wannan matakin ne a matsayin martani ga harin sama kan hasumiyar sadarwa a yankin Sirik.
Rundunar Kare Juyin Juya Hali a ci gaba ta bayyana cewa wannan hari, gargaɗi ne mai tsanani ga maƙiyin Amurka na dakatar da yunkurin kawo hari ta sama da ayyukan fataucin mai a mashigar Hormuz.
A cikin wannan sanarwa an kuma nanata cewa rundunar sararin samaniya ta Rundunar Kare Juyin Juya Hali a shirye take tsaf wajen mayar da martani ba tare da iyakacin yanayin ƙasa ba idan an sake kai mata hari.
Rundunar ta kuma yi gargaɗi cewa kamfanonin da suka keta doka da ke tafiya a hanyar maƙiyi, za su fuskanci matakai da hukunci mafi tsanani.
Daren jiya ma kamfanin dillancin labarai na hukuma na Jamhuriyar Islama ta Iran (IRNA) ya ba da rahoton cewa birnin Sirik da ke lardin Hormozgan da ke kudancin Iran, ya fuskanci harin sama na maƙiya.
Bisa ga wannan rahoto, harin yana da yanayin soji, amma ba a wallafa ƙarin cikakkun bayanai kan girman barna ko asarar rayuka da ya iya faruwa ba.
..............................
Ra'ayinka