25 Janairu 2020 - 18:24
Sakon Jagora Zuwa Ga Dalibai Na Kasashen Turai

A cikin sakon nasa Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, abubuwa da suke faruwa a halin yanzu a duniyar musulmi na nuni da wani sabon canji da ake samu.

Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ABNA24- ta rawaito Shafin yada labarai na ofishin jagora ya bayar da sanarwar cewa, an karanta sakon jagora a taron kungiyoyin daliban jami’a musulmi a kasashen a birnin Vienna na kasar Austria.

A cikin sakon ya ce; a zamanku da ke gudana a karo na hamsin da hudu a wanann shekara, abubuwa da dama sun waka a cikin kasashen musulmi da suke nuni da gagarumin canji da ake samu a duniyar musulmi.

A jamhuriyar muslucni ta Iran, abubuwan da aka gani a wannan shekara sun hada da shahada, karuwar karfin soji, ci gaba a dukkanin bangarori na ilimi, na addini da kuma na ruwa a bangarori daban-daban, da kuma kara yin tsayin daka wajen kare manufofi juyi, wanda fitowar al’umma ke nuni da hakan, musamman ma matasa, duk wannan na daga cikin abubuwa da suke nuni da gagarumin sauyi da yake tafe a duniyar msuulmi.

Haka nan kuma da yardar Allah da karfin ikonsa, da wannan ne al’ummar msuulmi za ta kai ga samun nasara wajen dawo da martabar addininta a duniya.

Ya kamala bayaninsa da cewa; tsarkake zuciya da kuma dogaro da Allah a cikin dukkanin lamurra, shi ne babban sirrin samun nasara a cikin dukkanin lamarran al’ummar musulmi.