23 Janairu 2020 - 18:03
Iran Za Ta Mayar Da Martani  Akan Duk Wata Barazana

Iran tace ;za ta mayar da martani da makaman da su ka dace akan duk Wata darazana

ABNA24-Ministan tsaro na Iran Birgediya Amir Hatami ya bayyana haka, yana mai jaddada cewa; kasar tana da wadataccen karfin da za ta iya mayar da martani akan duk masu wuce gona da iri.

Da yake Magana akan mayar da martanin da Iran ta yi akan kisan Janar Kassim Sulaimani da Amurka ta yi, Birgediya Hatami ambato bayanin jagoran juyin musulunci wanda ya bayyana harin da cewa; mari ne kawai,amma dole ne Amurka ta fice ta bar wannan yankin.”