-
Sakon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ga Taron Cika Shekaru 100 Da Sake Kafa Makarantar Hauza Ta Qum
Ayatullah Khamenei: Aikin makarantar hauza shi ne kafa manyan layukan da suka shafi sabuwar wayewar Musulunci/Bayyana abubuwan da ake bukata na babbar makarantar hauza a cikin al'ummar musulmi.
-
Qassam Sun Kai Munanan Hare-haren Kan Sojojin Isra'ila
Mummunan fashewar a Rafah ta faru ne akan Sojojin yahudawan sahyoniya wanda biyu daga ciki duka mutu nan take biyar suka jikkata 7
-
Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Iyalan Shahidan Qudus Na 2025
Da yammacin ranar Laraba 9 ga Zulqa’ada 1446 (7/5/2025) Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya gana da iyalan Shahidan waki’ar Quds din bana, a munasabar cikansu kwanaki 40 da Shahada, a gidansa da ke Abuja.
-
Rahoton Cikin Hotuna / Gidan Tarihi Na Imam Ali (AS) Da Ke Qum
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bayt As – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: a kwanan baya ne aka gina gidan tarihin Imam Ali (AS) a birnin Qum mai alfarma. Yana kunshe da kayan tarihi masu kima na tsoffin makamai, kamar takubba da bindigun gida, zane-zane na fasaha, kayan ado, zane-zane na Musulunci masu ban mamaki, da sauran dadaddun rubuce-rubucen littafin Allah Madaukakin Sarki da sauransu.
-
Yemen Ta Kai Hari A Filin Jirgin Saman Ramon Da Wani Muhimmin Wuri A Jaffa/Cikakkun Bayanai Na Faduwar Jirgin Yakin Amurka F-18
Dakarun kasar Yemen sun kai farmaki tashar jiragen sama na Ramon na Isra'ila da kuma jirgin Amurka Truman a wasu jerin hare-haren soji, kafin Amurka ta sanar da dakatar da kai hare-hare kan kasar Yemen.
-
Pakistan A Musayar Wuta Tsakaninta Da Indiya, Ta Tabbatar Da Kame Sojoji Da Kabo Jiragen Sama.
Kakakin rundunar sojin Pakistan na cewa, an tafka ruwan bama-bamai a wurare da dama na kan iyakar kasashen biyu, a yayin da hukumar ta ambato sojojin Indiya na cewa fararen hula 10 ne suka mutu yayin da wasu 35 suka jikkata a harin da Pakistan ta kai a yankin Kashmir.
-
Ansarullah: Isra'ila Ta Tsallake Jajayen Layi, Tabbas Ta Jira Martanin Yemen.
Mamba a ofishin siyasa na kungiyar Ansarullah ta Yaman a martanin da yake mayarwa kan hare-haren da gwamnatin sahyoniyawa ta ke kai wa wannan kasa a yau ya ce: Sahayoniyawa sun tsallaka jajayen layi, kuma tabbas su jira martanin Yemen.
-
Isra'ila Ta Harba Bama-Bamai A Filin Jirgin Saman Sana'a + Bidiyo
Rundunar sojin Isra'ila ta ce filin tashi da saukar jiragen saman ya daina aiki gaba daya, inda suka zargi Houthis da amfani da shi wajen safarar makamai.
-
Maƙarƙashiyar Duniya "Mantawa Da Palastinu" Tare Da Haɗin Bakin Sarakunan Larabawa
Hujjatul Islam Jawad Naqwi ya karkare da cewa: Mantawa da Palastinu laifi ne; yin watsi da raunukan Gaza laifi ne; kau da kai daga kofofi da katangar masallacin Al-Aqsa laifi ne. Kuma idan wani talaka farar hula ne ya aikata wannan laifi, za a iya gafarta masa; Amma idan ya fito daga malamin addini, mai mulki, mai yada labarai, mai tunani, malamin jami'a, jami'in gwamnati, ko dan siyasa, wannan cin amana ba zai yuwu a gafarta shi ba.
-
Iran: Jan Layinmu A Bayyane Ya Ke/Muna Tattaunawa Ne Kawai Akan Batun Nukiliya
Mai magana da yawun gwamnatin Iran ta tabbatar da cewa Tehran ta bayyana kudurinta na bin tafarkin diflomasiyya, kuma ta nuna xwannan kuduri a aikace, sannan ta nanata cewa dole ne daya bangaren ya nuna kyakkyawar niyyarsa.
-
Ma'aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Mayar Da Martani Ga Munanan Zarge-Zargen Da Ake Yi Wa Tehran Dangane Da Ayyukan Sojin A Kasar Yemen.
A cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar ta bayyana cewa, zarge-zargen da ba su da tushe balle makama da ake ci gaba da danganta mata na jarumtakar al'ummar kasar Yemen wajen kare kai da goyon bayan al'ummar Palastinu ga Iran wani cin fuska ne ga wannan al'umma da ake zalunta.
-
Fursunonin Gidan Yarin Hillah Na Lardin Babil Sun Tsere, Ana Ci Gaba Da Bincike A Kansu
Iraki ta bayar da sanarwar tserewar fursunoni daga gidan yarin Hillah na lardin Babil, tare nemansu ruwa a jallo
-
Aikin Hajji Manhaja Ce Ta Wayewar Musulunci, Kuma Hanya Ce Ta Tabbatar Da Al’umma Daya Dunkulalliya.
Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya da yake jaddada fa’idar aikin Hajji da damarmakin da ke cikinsa, ya dauke ta a matsayin dandali ne na tabbatar da al’ummar musulmi, ya kuma yi kira da a zurfafa amfani da wannan aiki na gina wayewa daga manyan mutane, jami’ai, da mahajjata.
-
Dakarun Yaman Sun Sanar Da Fara Hana Jiragen Isra'ila Ta Shi A Ko Ina
Sojojin Yaman sun fitar da wata sanarwa inda suka sanar da cewa za su kai hare-hare akai-akai kan filayen saukar jiragen sama na Isra'ila tare da katangewa ta sama kan gwamnatin kasar da nufin tallafawa al'ummar Palastinu.
-
Labarai Cikin Hotona | Yadda Mazauna Tulkarm Su Kai Gudun Hijira Biyo Bayan Gargadin Sojojin Sahayoniya
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: dakarun gwamnatin sahyoniyawan sun ci gaba da kai hare-hare kan birnin Tulkarm da sansanonin sa na tsawon watanni kusan uku a ci gaba da fafatawa a fili tare da kaddamar da hare-hare da gargadin ruguza gidajen Palastinawa. A cikin sa'o'i 24 da suka gabata 'yan mamaya na yahudawan sahyuniya sun ba da umarnin rusa gidaje da gine-gine 106 na Palasdinawa a sansanonin 'yan gudun hijira na Tulkarm da Nur Shams.
-
Sheikh Ibrahim Zakzaky Ya Jaddada Muhimmiyar Rawar Da Kafafen Yaɗa Labarai Ke Takawa Wajen Inganta Koyarwar Ahlul Baiti (AS).
Ci gaba da kawo cikakken rahoton babban taron kasa da kasa na Kamfanin Ahlul-baiti (AS) na kasa da kasa karo na uku, tare da halartar masu fafutuka daga kasashen Afirka sama da 20 + hotuna da bidiyoyi.
-
Imam Khamene'i: Idan Da Al'ummar Musulmi Sun Kasance Kansu A Haɗe, Da Bala'in Palastinu Da Gaza Ba Su Faru Ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce da a ce al'ummar musulmi sun kasance masu hadin kai, da musibar Palastinu da Gaza ba su faru ba, kuma da kasar Yemen ba ta fuskanci irin wannan matsin lambar ba.
-
Kungiyoyin Gwagwarmayar Sun Yaba Da Jinjina Harin Yamen Ga Isra'ila
Kungiyar Hizbullah da kwamitin Falasɗinawa da Kungiyar Hamas sun yaba da harin makami mai linzami da sojojin Yaman suka kai kan filin jirgin saman Ben Gurion
-
Yamen Ta Kai Hari Ga Filin Jirgin Ben Gurion Na Isra'ila+ Bidiyo
Majiyoyi na yaren Hebrew sun ba da rahoton cewa an yi ta jin karar ƙararrawa a Tel Aviv, biyo bayan harin da Yamen ta kai kan filin jirgin Ben Gurion.
-
Sheikh Ibrahim Alzakzaky (H): Ka Gyara Kanka, A Ga Addinin Daga Wajenka, Ya Fi Ma Ka Yi Magana
Jagora ya dauki lokaci yana bayani dangane da ma’anar Jihadi. Yace: “Ana cewa Danfodiyo, za su ce “Jihadi”. Har nakan ce ku gane fa, Jihadin nan ba yana nufin daukan takobi ba ne, yana farawa da kai kanka ne ka yi “jihadun nafs”, ka siffantu da addini tukunna, su ganshi a jikinka sannan kuma ka kira wasu”.
-
Ayatullah Ramezani: Jihadi A Fagen Yaɗa Labarai Bai Gaza Jihadi A Zahiri Ba
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: a safiyar yau ne aka gudanar da taron kasa da kasa karo na uku na "masu yaɗa labaran Ahlulbaiti (AS)" bisa munasabar kwanaki goma na karama tare da halartar masu fafutuka da masana daga Iran da nahiyar Afirka tare da ɗaukar nauyin kamfanin dillancin labarai na Ahlul Baiti (AS) - ABNA, a zauren majalissar Ahlul-bayt (AS).
-
Yemen Takai Harin Makamai Mai Linzami A Yankunan Da Aka Mamaye /Lieberman: Ba Mu Da Tsaro
A yayin da majiyoyin yahudawan sahyuniya suka bayar da rahoton cewa, sojojin kasar Yemen sun sake harba makamai masu linzami tare da jin karar kararrawar gargadi a arewacin yankunan da aka mamaye, tsohon ministan yakin haramtacciyar kasar Isra'ila, ya yi kakkausar suka kan ayyukan majalisar ministocin gwamnatin kasar, inda ya yi la'akari da yanayin tsaro a matsayin wani bala'i.
-
Bidiyon | Taron Ƙasa Da Ƙasa Karo Na 3 Na Masu Ayyukan Yaɗa Labaran Ahlulbaiti (AS) Tare Da Halartar Masu Fafutukar Yada Labarai Na Nahiyar Afrika
Cikakken rahoton taro na uku na kasa da kasa na maruwaitan yada labaran Ahlulbaiti (AS) tare da halartar masu fafutuka daga kasashen Afirka sama da 20 + hotuna da bidiyoyi.
-
Hotuna | Taron Ƙasa Da Ƙasa Karo Na 3 Na Masu Ayyukan Yaɗa Labaran Ahlulbaiti (AS) Tare Da Halartar Masu Fafutukar Yada Labarai Na Nahiyar Afrika - 3
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: a safiyar yau ne aka gudanar da taron kasa da kasa karo na uku na "masu yaɗa labaran Ahlulbaiti (AS)" bisa munasabar kwanaki goma na karama tare da halartar masu fafutuka da masana daga Iran da nahiyar Afirka tare da ɗaukar nauyin kamfanin dillancin labarai na Ahlul Baiti (AS) - ABNA, a zauren majalissar Ahlul-bayt (AS).
-
Hotuna | Taron Ƙasa Da Ƙasa Karo Na 3 Na Masu Ayyukan Yaɗa Labaran Ahlulbaiti (AS) Tare Da Halartar Masu Fafutukar Yada Labarai Na Nahiyar Afrika - 2
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: a safiyar yau ne aka gudanar da taron kasa da kasa karo na uku na "masu yaɗa labaran Ahlulbaiti (AS)" bisa munasabar kwanaki goma na karama tare da halartar masu fafutuka da masana daga Iran da nahiyar Afirka tare da ɗaukar nauyin kamfanin dillancin labarai na Ahlul Baiti (AS) - ABNA, a zauren majalissar Ahlul-bayt (AS).
-
Bom Ya Tashi A Damascus / Tel Aviv Ta Kai Hari A Fadar Shugaban Ƙasa
An kai harin na Isra'ila a nisan mita 400 daga fadar shugaban kasa da ke Damascus.
-
Hotuna | Taron Ƙasa Da Ƙasa Karo Na 3 Na Masu Ayyukan Yaɗa Labaran Ahlulbaiti (AS) Tare Da Halartar Masu Fafutukar Yada Labarai Na Nahiyar Afrika - 1
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: a safiyar yau ne aka gudanar da taron kasa da kasa karo na uku na "masu yaɗa labaran Ahlulbaiti (AS)" bisa munasabar kwanaki goma na karama tare da halartar masu fafutuka da masana daga Iran da nahiyar Afirka tare da ɗaukar nauyin kamfanin dillancin labarai na Ahlul Baiti (AS) - ABNA, a zauren majalissar Ahlul-bayt (AS).
-
Araghchi: Za A Gudanar Tattaunawa Zagaye Na Gaba A Roma
Ministan harkokin wajen Iran ya sanar da cewa, za a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa ba ta kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka dangane da shirin nukiliyar Iran da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata a birnin Rome.
-
Hotuna | Yadda Gobara Ta Tashi A Yankunan Da Isra'ila Ta Mamaye
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: wata gobara na ci gaba da bazuwa a tsaunukan birnin Kudus da aka mamaye, kuma an kwashe wasu mazauna yahudawan sahyoniya da ke cikin wadannan yankuna da aka mamaye sakamakon bazuwar wutar.
-
Hotuna: Yara A Khan Yunis Sun Buƙaci Kawo Ƙarshen Hare-Haren Ta'addancin Isra'ila
Kamfanin dillancin labaran AhlulBaiti: Yara a birnin Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza sun yi kira da a kawo karshen laifukan ta'addancin gwamnatin sahyoniyawa a wani gangami mai taken "Dakatar da yaki da kisan kare dangi da zalunci". Yara da suke dauke da tutoci masu taken "Badon Mutuwa Ba, Bafon Yunwa Ba". yaran sun yi jawabi ga al'ummomin duniya: "Muna mutuwa saboda tashin bamabamai, cututtuka, yunwa da kishirwa, kuma duniya ta yi shiru".