26 Yuni 2025 - 23:03
Source: ABNA24
Jagora: Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Mangari Amurka Mangari Mai Tsanani + Video

A cikin sakon bidiyo na uku, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya taya al'ummar Iran mai girma murna kan nasarar da suka samu kan gwamnatin yahudawan sahyoniya da Amurka a yakin da suke yi da kasar.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: a cikin sakon bidiyo na uku, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yaba da irin hadin kai da hadin gwiwar al'ummar Iran mai girma tare da taya murna kan nasarar da gwamnatin Iran ta samu kan yahudawan sahyoniya da Amurka a yakin da suka yi a kan kasar.

Nassin sakon Jagoran juyin juya halin Musulunci shi ne kamar haka;

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai

بسم الله الرّحمن الرّحیم

Amincin Allah ya tabbata ga al'ummar Iran abar kauna kuma mai girma. Da farko ina girmama shahidai masu daraja da suka yi shahada a baya-bayan nan; Janarorin shahidai, masana kimiyya shahidai wadanda suke da kima sosai bisa gaskiya da adalci wadanda su kai aiki ga Jamhuriyar Musulunci, kuma a yau in Allah ya yarda za su sami ladan ayyukan da suka yi na musamman a wajen Ubangiji.

Ina ganin ya zama dole in taya al'ummar Iran murna. Ina so in taya murna daban-daban ga al'umma:

Na farko, taya murna kan nasarar da aka samu kan gwamnatin sahyoniya ta kama karya. Gwamnatin Sahayoniya da duk wannan hayaniyar da ta ke da, da dukkan wadannan da'awarta, ta kusa rugujewa da murkushe su a karkashin hare-haren Jamhuriyar Musulunci. Tunanin cewa za a gwamnatin Jamhuriyar Musulunci zata iya yin irin wadannan nau'o'in hare-hare msu muni, bai shiga cikin kwakwalwarsu da tunaninsu ba, amma kuma hakan ya faru. Mun gode wa Allah da Ya taimaki sojojin mu, suka samu nasarar tsallake duk wani tsrain tsaron masu ci gaba da yawa tare da rusa da yawa daga cikin garuruwansu da wuraren tsaron soji da makamai masu linzami sojojinmu da harin makamai masu tsananin karfi! Wannan yana daga cikin mafi girman ni'imomin Allah; wannan yana nuna cewa gwamnatin sahyoniyawa ta san cewa kai hari kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran yana da tsada a gare ta, zai haifar mata da tsadar rayuwa, da haifar mata da biyan farshi mai tsada. Kuma alhamdulillahi wannan ya faru; Daraja da alfahari sun tabbata ga sojojinmu da al’ummarmu maus daukaka da suka kirkiri wadannan runduna daga cikin su, suka horar da su, suka tallafa musu, suka samar da kuma karfafa hannayensu (karfi) don gudanar da wannan gagarumin aiki.

Taya murna ta biyu tana da nasaba da nasarar da abin kaunarmu Iran ta samu kan gwamnatin Amurka. Gwamnatin Amurka ta shiga yaki kai tsaye domin tana jin cewa idan ba ta shiga ba, to za a ruguza gwamnatin sahyoniya gaba daya. Ta shiga yakin ne don ceto ta, amma bata cimma wani muhimmin abu ba. Sun kai hari kan cibiyoyin mu na nukiliya - wanda ba shakka ya cancanci tuhumar laifuka a kotunan duniya - amma sun kasa yin wani abu mai mahimmanci. Shugaban Kasar Amirka (1) wajen bayanin abun da ya faru ya wuce gona da iri ta hanyar da ba a saba gani ba, ya zama cewa yana buqatar wannan wuce gona da iri ne; duk wanda ya ji wadannan kalmomi ya fahimci cewa akwai wata gaskiya a karkashin wadannan kalmomi. Ba su iya yin komai, ba za su iya cimma burinsu ba, suna wuce gona da iri ne don rufe gaskiya. A nan ma jamhuriyar Musulunci ta yi nasara, sannan kuma Jamhuriyar Musulunci ta yi wa Amurka mangari mai tsanani a kuncinta. Ta kai hari a daya daga cikin muhimman sansanonin Amurkawa a yankin, sansanin Al-Udeid, inda ta yi barna. Mutanen da suka yi karin gishiri a cikin lamarin sun yi kokarin rage girman lamarin, don su ce babu abin da ya faru, lokacin da wani babban lamari ya faru. Kasancewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana iya kaiwa ga wasu muhimman cibiyoyi na Amurka a wannan yanki, kuma za ta iya daukar mataki a kansu a duk lokacin da ta ga ya dace, ba karamin lamari ba ne, lamari ne babba, kuma za a iya maimaita wannan lamari a nan gaba; to idan kuwa an kai harin, to tabbas farashin abokan gaba da wanda ya keta iyaka zai zama yana da yawa.

Taya murna ta uku ita ce taya murna kan irin hadin kai da hadin gwiwar al'ummar Iran. Alhamdu lillahi al’ummar kasa mai kusan yawan al’umma miliyan casa’in, cikin hadin kai, murya daya, kafada da kafada, a gare da juna ba tare da wani bambanci ba a cikin bukatu da manufar da suke bayyanawa amma sun tsaya tsayin daka, tare da rera take daya, da magana daya, suna masu goyon bayan ayyukan jami’an tsaro, kuma irin hakan zai kasance daga yanzu anan gaba. Al'ummar Iran sun nuna irin girman da suke da shi, da irin matsayinsu na fice a cikin wannan lamari tare da nuna cewa idan ya zama akwai bukata za a ji murya guda daga wannan al'umma, kuma alhamdulillahi hakan ya faru.

Batun da nake son bayyanawa a matsayin wani muhimmin batu na bayanai na, shugaban Amurka ya fada a daya daga cikin maganganunsa da bayanansa cewa dole ne Iran ta mika wuya. "Su mika wuya"! yan ba batun hana wadatar sinadari ba ne kuma, ba batun masana'antar nukiliya ba ne, yanzu batu ne na Iran ta mika wuya. Tabbas wannan kalma ce babba da shugaban Amurka zai iya furtawa. Iran mai girma, Iran mai wannan dinbin tarihin, Iran mai wannan tarin al'adun, Iran mai irin wannan azama ta kasa, ya zmai an anbaci sunan "mika wuya" ga irin wannan kasa abin izgili ne ga wadanda suka san al'ummar Iran. Amma maganarsa ta bayyana wata gaskiya; Tun farkon juyin juya halin Musulunci, Amurkawa sun shiga rikici da Iran din Musulunci, kuma a duk ko wane lokacin suna zuwa da fakewa da wani uzuri: a wani lokacin kan batun Hakkin dan Adam, a wani kuma kan kare dimokuradiyya, a wani karon kuma kan hakkin mata, a wani karan kan batun wadatar sinadarai, wani lokacin kuma kan batun nukiliya, a wani kuma kan kera makamai masu linzami; suna fakewa da uzuri iri-iri, amma ainihin lamarin ba wani abu ba ne face abu guda, wato "Mika kain Iran". Wadanda suka gabata ba su fadi haka ba, domin wannan abu ne da ba za a yarda da shi ba; ba abu ne da za’a yarda da shi ko amincewa ba a cikin wani tunani na dan Adamwai a cewa wata al'umma su mika wuya, don haka suka boye hakan a karkashin wasu batutuwa. Wannan mutumin ya fallasa wannan gaskiyar, ya nuna ta kuma ya bayyana cewa Amurkawa za su gamsu ne kawai da mika wuyar Iran ba komai ba. Kuma wannan batu ne mai mahimmanci! Ya kamata al'ummar Iran su sani cewa wannan shi ne (dalilin) ​​adawa da Amurka, kuma wannan babban cin mutuncin al'ummar Iran shi ne Amurkawa suke da, kuma irin wannan lamari ba zai taba faruwa ba; ba zai taba faruwa ba.

Al'ummar Iran al'umma ce mai girma, Iran kasa ce mai karfi da fadi, Iran tana da dadadden wayewa; wadatar al'adu da wayewarmu ta fi Amurka da makamantanta sau ɗari. Ya zamo wani ya yi tsammanin Iran ta mika wuya ga wata kasa hakan na daga cikin irin wadannan shirme na karya wadanda ko shakka babu za su zama abin izgili ga masu hikima da ilimi. Al'ummar Iran madaukaka ne kuma za su kasance cikin daukaka, ta kasance mai nasara kuma za ta yi nasara, da yardar Allah. Kuma muna fatan Allah madaukakin sarki ya kiyaye wannan al'umma da ke karkashin inuwar falalarsa da daraja da daukaka, ya daukaka darajar Imaminmu mai girma, kuma ya sanya Shugaba Bakiyyatullah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya zama mai yardewa ga wannan al'umma, kuma taimakonsa ya ya zamo a bayan wannan al'umma.

والسّلام علیکم و رحمة‌الله و برکاته

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha