Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul bayt As ABNA ya habarta cewa, a safiyar jiya Asabar ne aka fara gudanar da jana’izar shahidan a hukumance, inda aka fara bude taron da karatun aya ta 38 a cikin suratul Hajji.
Jerin gwanon da suka kunshi shahidai bangarori daban-daban na al'ummar Iran da suka hada da yara, mata, malamai, shugabanni, da sauran shahidai. An fara shi ne da karfe 8:00 na safe daga dandalin juyin juya halin musulunci zuwa dandalin 'yanci. Maidani Inqilab da zuwa Maidan Azad
Tun da sanyin safiya, dandalin juyin juya halin Musulunci ya cika da dimbin jama'a, suna daga jajayen tutocin Imam Husaini (a.s). Da ke bayyana taken da aka rubuta da hannu na adawa da sahyoniya da Amurka domin nuna kyama ga laifuffukan ta’addanci da suka tafka a ga rayuka da zukatan al'ummar musulmi a cikin 'yan makonnin nan, musamman a lokacin yakin kwanaki 12 da aka yi.
Wadannan taruka sun zama siffa ta musamman na hadin kan kasa da za su kasance a cikin tarihin kasar wanda Jama'a da dama ne suka halarci jana'izar shahidai 60 da Isra'ila ta aiwatar a Tehran babban birnin kasar Iran. Haka kuma gungun masu makoki daga Bahrain, Iraki, da sauran kasashen Larabawa sun halarci taron.
Bayan kammala jana'izar, za a binne gawarwakin a wurare masu tsarki a Tehran, Behisht Zahra’a As, da sauran garuruwa.
Mahalarta Muzaharar Jana'izar sun yi ta rera cewa, "Labbaik Ya Husain"
Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Masoud Pezeshkian ya halarci jana'izar shahidan a dandalin juyin juya halin Musulunci na birnin Tehran.
Kwamandan hedikwatar Khatamil-Anbia Manjo Janar Gholam Ali Rashid da dansa Amin Abbas Rashid sun yi shahada a harin farko da gwamnatin sahyoniyawa ta kai a Tehran babban birnin kasar Iran a safiyar Juma'a.
Inda hanyoyi da ababen hawa da tashar jirgin kasa suka Tehran cika makil da 'yan kasar da ke tururuwa zuwa dandalin juyin juya halin Musulunci domin halartar jana'izar kwamandojin shahidai da sauran wadanda suka yi shahada a hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin sahyoniya ta kai kan kasar Iran din a baya-bayan nan.
An kawata bangon dandalin juyin juya halin Musulunci da ke birnin Tehran da hotunan shahidan wuce gona da iri na mujrimar gwamnatin sahyoniyawa.
Your Comment