28 Yuni 2025 - 08:27
Source: ABNA24
A Yau Ne Ake Gudanar Da Jana’izar Shahidan Yakin Da Iran Ta Yi Da Isra’aila A Tehran + Bidiyoyi

Kamar yadda a hukumce aka sanar da gudanar da jana’izar gawawwakin shahidan da gwamnatin sahyoniyawa ta shahadantar a yakin da aka kakabawa Iran a safiyar yau Asabar 28/06/2025 ya zuwa yanzu ayarin da ker dauke da gawarwarkin sun isa dandalin Enghelab

Za a gudanar da rakiyar jana’izar ne daga dandalin Enghelab zuwa dandalin Azadi

Cikakken Bayani Akan Yadda Da Guraren Inda Za’a Yi Jana'izar Shahidan Da Wuraren Da Za’a Binne Su:

1- Sardar Hassanzadeh kwamandan rundunar IRGC ta Tehran ya bayyana dangane da wuraren da za’a binne wadannan shahidan: Mafi yawan kwamandojin za a binne su ne a Beheshti-Zahra, sauran kuma za a binne su a Imamzadeh bisa wasiyyarsu.

Jana'izar kwamandojin shahidai kamar haka:

1- Shahid Salami da Shahida Shane'i, Shahidai Rabbani da iyalansa

- Za’a binne shi a hubbaren Sayyidina Abdulazim, Lahadi, karfe 8:00 na safe

2- Shahidi Muhammad Bagheri da Shahida Mehrabi

- Za’a binne shi a kusa da Shahidi Hassan Bagheri a bangare mai na 24 na Behesht Zahra (AS)

3- Shahid Shadmani

- Taron bankwana: daren Asabar a Husainiyar Shahidan Hamedan.

- Taron jana'izar: Lahadi 28 ga Yuli 2025, a makabartar Shahidai ta Hamedan.

4- Shahid Mahmoud Bagheri da Shahida Hajizadeh

- Jana'izar: Asabar 27 ga Yuli 2025, Tehran

- Za’a binne su a bangare mai namba 50 a cikin masu kare haramin

5- Shahidi Rashid

- Jana'izarsa: Asabar 27 ga Yuli, 2025 Tehran

- Za’a binne shi a Gulzar Shuhada Dizful

6- Shahidi Tehranchi da Shahid Fereydoun Abbasi

- Jana'izar: Asabar 27 ga Yuli, 2025 Tehran. Za a bizne Shahidi Tehranchi da karfe 1:00 na ranar yau a hubbaren Sayyidina Abdulazim.

7- Shahidi Muhammad Kazemi

- Jana'izar: Asabar, Yuli 27, a Mashhad mai tsarki

8- Shahidi Muhammad Reza Nasir Baghban

- Jana'izar: Asabar 27 ga Yuli, Tehran

- Binnewa: A cikin bangare na 24 kusa da tsohon abokinsa, Sardar Haj Rahimi

9- Shahid Haj Ramadan

- Jana'izarsa: Asabar 27 ga watan Yuli tare da sauran kwamandojin shahidai a Tehran, Litinin 28 ga watan Yuli a mahaifarsa a birnin "Sonqor Kliai" (lardin Kermanshah), da kuma ranar Alhamis 03 ga watan Julai a birnin Qum mai tsarki.

- Binnewa: 12 ga July, a Qum, hubbaren Sayyidah Ma’asumah (AS)

10- Shahidi Nekoei

- Jana'izar: Asabar 27 ga Yuli, Tehran

- Za’a binne shi a Shiraz

11- Shahid Shahriari

- Jana'izar: Asabar 27 ga Yuli, Tehran

- Za’a bine shi: A Imamzadeh Saleh Tajrish

Your Comment

You are replying to: .
captcha