23 Yuni 2025 - 18:29
Source: ABNA24
An Gano Ƙanana Jiragen Ƙunar Baƙin Wake Sama Da 10,000 Tare Da Tarwatsa Cibiyar Ƴan Leƙen Isra'ila A Tehran 

A ci gaban binciken tsaro a cikin kwanakin nan runduna tsaron Iran ta gano wata cibiyar ƴan amshin shatan Isra'ila tare samun su da sama da jiragen Ƙunar Baƙin Wake 10,000 a Tehran 

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA - ya habarta cewa: jami'an sanar da cewa galibi jiragen ana anfani da su wajen leken asiri da aikin zagon ƙasa ta hannun ƴan barandar da ke da alaƙa da Isra'ila. 

Sannan kuma an kama wata cibiyar aikewa da jiragen a arewacin Tehran inda mai magana da yawun Ƴan Sanda: An gano cibiyar aikewa da jiragen kunar bakin wake a tsaunukan da ke kusa da arewa maso yammacin Tehran tare da kama masu aikewa da jiragen. A cikin wannan aikin, an gano adadi mai yawa na na'urorin sarrafawa da kayan aikin jiragen kuma an kama 2 mutane biyu a wannan sumamen.

Your Comment

You are replying to: .
captcha