Kamfanin dillancin labaran Ahlul Baiti (ABNA) ya bayar da rahoton cewa, harin makami mai linzami da Iran ta kai kan matatar mai ta Haifa da ke tashar jiragen ruwa ta Haifa ya dakatar da gudanar da ayyukan wannan cibiyar mai na Isra'ila tsawon watanni tare da girgiza kayayyakin makiya.
Jaridar Times of Israel, ta nakalto kamfanin da ya mallaki matatar mai ta Bazan, ta ruwaito cewa matatar mai ta Haifa da ta lalace a lokacin harin da Iran ta kai, mai yiwuwa ta ci gaba da gudanar da ayyukanta gaba daya nan da ‘yan watanni, nan da watan Oktoba.
A baya an ba da rahoton cewa an yi barna mai yawa a kan kayayyakin kamfanin na Bazan biyo bayan harin makami mai linzami da Iran ta kai a daren 16 ga watan Yuni.
A cewar jaridar, Kamfanin na Bazan ya sanar a wani rahoto da ya aikewa hukumar da ke sa ido kan yadda ya ci gaba da gudanar da ayyukansa a hankali, kuma mai yiyuwa ne zuwa watan Oktoba kafin ya fara aiki gadan-gadan.
Tun da farko, kafar yada labaran yahudawan sahyoniya ta Isra'ila "Kan" ta bayar da rahoton cewa, matatar mai na kamfanin Bazan da ke tashar jiragen ruwa na Haifa ta daina aiki bayan da wani makami mai linzami na Iran ya afkawa tashar samar da wutar lantarki.
Kafar yada labaran Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kuma tabbatar da cewa Iran ta kai harin makami mai linzami kan matatar mai. Wadannan hare-haren dai wani bangare ne na mayar da martani mai muni ga gwamnatin sahyoniyawa da take kai wa Iran hari tun daga ranar 13 ga watan Yuni, wanda ya kasance tare da kaddamar da "Alkawarin Gaskiya Na Uku", inda aka kai hare-hare masu muhimmanci a dukkan yankunan da aka mamaye da makamai masu linzami na Iran. Bayan harin wuce gona da irin na yahudawan sahyoniya da yayi sanadiyyar shahadar wasu kwamandojin soji da fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, da kuma masana kimiyyar nukiliyar Iran.
Your Comment