Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarto maku cewa: bisa rahotannin da suke zuwa hareh-haren Iran sun samu wurare da dama a Isra’ila kamar birnin Nas Zayuna kudancin Tal Aviv da Ramat Ghan da cikin Tal Aviv da yankin Karmal d ake Haifa.
A wasu ruwayoyin Iran ta harba makamai masu linzami 30 a lokaci guda kuma mafi yawansu sun kai ga hadafin da aka nufata da su wanna harin dai na biyowa bayan harin da Amruka ta ce ta kai ne ga Cibiyoyin Nukiliyar Iran guda uku a daren jiya.
Biyo bayan wadannan makamai kuma Iran ta kara aika wasu guda goma ba tare da kakkautawa ba in da aka ji karar fashewa a gurare da dama a Akka Gaulan da Haifa. Bisa rahoton da jaridar Hayum ta Isra’la ta bayar tace wani yanki da ke bakin tekun gaba daya an tarwatsa shi.
Your Comment