(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya Ayatollah Sistani ya aike da rubutaccen sakon ta’aziyyar shahadar Janar Qassem Sulaimani zuwa ga jagoran juyin juya hali Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.
A cikin wasikar Ayatollah Sistani ya bayyana cewa, samun labarin shahadar bababn gwarzo Haji Qassem Sulaimani ya saka mu cikin bakin ciki matuka.
Hakika ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen fatattakar mayakan ‘yan ta’addan Daesh daga Iraki, ya yi gagarumin aiki da hidima mai yawa ga Iraki tsawon shekaru, wanda al’ummar kasar ba za su taba mantawa da hakan ba.
Ina mika sakon ta’aziyya kan wannan baban rashi gare ka da kuma dukkanin iyalansa da al’ummar Iran baki daya, musamman al’ummar lardin Kerman.
/129