6 Janairu 2020 - 05:46
​ Iran : An Fara Ban Kwana Da Gawar Janar Shahid Qasim Suleimani

A Iran, an fara ban kwana da gawar babban kwamandan dakarun

(ABNA24.com) kare juyin juya halin musulinci na kasar, Janar Shahid Qasim Sulaimani, wanda

ya rasa ransa a harin saman da Amurka ta kai wa ayarin motocinsa da sanyin

safiyar ranar Juma’a data gabata a kusa da filin jirgin saman birnin Bagadaza.

Da yammacin jiya Asabar ne, aka isa da gawar ta Shahid Qasim Sulaimani a birnin Khouzestan, na Iran, kafin daga bisani a isa da ita a biranen Mashad, Qum sai kuma Tehran babban birnin kasar a gobe Litini, inda za’ayi masa jana’iza a hukumance tare da halartar manyan jami’an kasar ta Iran a sahun gaba jagoran juyin juya halin musulinci, Ayyatolah Sayyid Ali Khamenei.

Za’a binne gawar marigayin Shahin Qasim Sulaimani a mahaifarsa dake binrin Kerman.

Kafin hakan dama milyoyin al’ummar kasar Iraki ne, inda ya yi shahada, sukayi rakiyar ban kwana da shi da wasu manyan kwamandojin da sukayi shahada tare da shi da suka hada Abu Mahdi al-Muhandis.

A Irakin ma an zagaya da gawarwakin shahidan a biranen Bagadaza, Najaf, Kazemeyn da kuma Karbaba, inda milyoyin jama’a ke firta kallaman la’antar Amurka.



/129