2 Janairu 2020 - 05:34
Iran Ce Kadai Kasar Da Ba A Bin Ta Bashi A Duniya

Minista mai kula da shimfida hanyoyi na Iran ya bayyana haka yana mai kara da cewa; Ma’aunin tattalin arzikin Iran yana tafiya daidai, domin a halin yanzu kayan da Iran take fitarwa waje ya fi wanda ta ke shigo da su yawa.

(ABNA24.com) Minista mai kula da shimfida hanyoyi na Iran ya bayyana haka yana mai kara da cewa; Ma’aunin tattalin arzikin Iran yana tafiya daidai, domin a halin yanzu kayan da Iran take fitarwa waje ya fi wanda ta ke shigo da su yawa.

Muhammad Salami wanda ya kaddamar da wasu sabbin aikace-aikace na gwamnari a gundumar Ardebil a jiya Laraba ya kara da cewa; A karkashin takunkumi na zalunci da Amurka ta kakaba wa Iran, kasar tana zama wani babban kamfani da ake ci gaba da kere-kere a muhimman bangarori da su ka hada, na gine-gine, ruwa, wutar lantarki da kuma iskar gas.

Dangane da gidajen da gwamnati ta ke ginawa da sayar da su ga talakawa cikin rahusa, ministan ya ce; gwamnati za ta ci gaba da kokari domin kawo karshen duk wasu matsaloli da ake fuskanta a wannan fagen.



/129