(ABNA24.com) Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta sanar da cewa; Manyan jami’an tsaron kasashen Rasha, Afghanistan da India sun iso Tehran ne domin halartar taro a kan hanyoyin tabbatar da tsaro a cikin wannan yankin wanda shi ne irinsa karo na biyu.
Daga kasar Rasha shugaban hukumar tsaron kasar ne Nikolai Patrushev ne ya ke jagorantar tawagar jami’an tsaro, yayin da shugaban hukumar tsaron kasar Afghanistan Hamadullah Muhib ya jagoranci tawagar kasarsa. Daga kasar Indiya kuwa mataimakin shugaban hukumar tsaron kasar ne, Rajindar Khana ne ya iso tare da tawagar da take rufa masa baya.
Sauran kasashen da su ka turo da wakilai akan harkokin tsaro sun kunshi kasar China, da Tajikistan. Ana sa ran cewa wani jami’in tsaron daga kasar Uzbekistan zai iso nan gaba kadan
/129
18 Disamba 2019 - 05:58
Lambar labari: 994738
Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta sanar da cewa; Manyan jami’an tsaron kasashen Rasha, Afghanistan da India sun iso Tehran ne domin halartar taro a kan hanyoyin tabbatar da tsaro a cikin wannan yankin wanda shi ne irinsa karo na biyu.