15 Disamba 2019 - 05:45
An Gayyaci Wani Limami Da Ya Fassara Kur’ani Bisa Kure A Masar

Bangaren kasa da kasa, an gayyaci limamin wani masallaci da ya fassara ayoyin kur’ani bisa kure a Masar.

(ABNA24.com) Shafin yada labarai na sadal balad ya habarta cewa, Sabri Ibadah mataimain ministan harkokin addini ya bayyana cewa a jiya an gayyaci limamin wani masallaci da ya fassara ayoyin kur’ani bisa kure a Masar a garin Tanta da ke cikin lardin Garbiyya a kasar.

Wannan mataki dai yana zuwa ne bayan da limamin ya fassara wasu ayoyin kur’ani a cikin hudubar juma’a bisa kure, wanda hakan ya dauki hankulan jama’a.

An nada wannan limami ne dai tun a kimanin shekaru ashirin da suka gabata, inda kuma yake gabar da huduba a kowace Juma’a, wanda hakan yasa cibiyar azhar ta nuna takaicinta da faruwar hakan.


/129