4 Disamba 2019 - 04:25
Shugaba Buhari Na Nijeriya Ya ce Babu Ranar Bude Iyakokin Kasar

A wani bayani da ya yi da manema labarai game da batun bude iyakokin Nigeria Shugaba Mohammadu Buhari ya bayyana cewa daga lokacin rufe iyakokin kasar ta kasa zuwa yanzu an samu ci gaba sosai, inda yawan amfani da man fetur da ake yi a cikin gida ya ragu da kaso 30% idan aka kwatanta shi da kafin rufe iyakokin, saboda fita da mai din da ake yi ta barauniyar hanya domin sayar da shi da tsada a kasashen makwabta.

(ABNA24.com) A wani bayani da ya yi da manema labarai game da batun bude iyakokin Nigeria Shugaba Mohammadu Buhari ya bayyana cewa daga lokacin rufe iyakokin kasar ta kasa zuwa yanzu an samu ci gaba sosai, inda yawan amfani da man fetur da ake yi a cikin gida ya ragu da kaso 30% idan aka kwatanta shi da kafin rufe iyakokin, saboda fita da mai din da ake yi ta barauniyar hanya domin sayar da shi da tsada a kasashen makwabta.

Ya ci gaba da cewa za’a bude iyakokin kasar ne idan al’amura sun daidaita, kuma ta dauki matakin ne domin hana shigo da shinkafa, man fetur da makamai ta barauniyar hanya kasar da hakan ke illata tattalin arzikin kasar.

A watan Oktoban da ya gabata ne babban baturen ( Controller General ) na hukumar costums na kasa kanar Hammed Ali mai ritaya ne ya sanar da haramata shiga ko fitar da wasu kayyakin ta iyakokin kasar Nigeria, a kokarin da gwamnati ke yi na sa ido sosai kan abubuwan da ke shiga ya fita a fadin kasar.

Matakin ya shafi kasashen Niger, Benin da ke makwabtaka da Nigeria da hakan ya jefa su cikin matsalar tattalin arziki saboda hana su shigar da hajojinsu cikin Nigeria.



/129