4 Disamba 2019 - 04:24
Iran Ta Bukaci Kasashen Turai Su Bayar Da Damar Shigar Da Maganin Cutar Fata Ta EB Da ke Addabar Yara Kanana

Manistan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif da yake mayar da martani a shafinsa na Twitter ya soki lamirin kasashen turai game da irin mataken da suke dauka kan yarjejeniyar da aka cimma kan shirin iran na nukliya.

(ABNA24.com) Manistan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif da yake mayar da martani a shafinsa na Twitter ya soki lamirin kasashen turai game da irin mataken da suke dauka kan yarjejeniyar da aka cimma kan shirin iran na nukliya.

Ya kuma nuna cewa kasashen turai 3 da Sweden da kugiyar tarayyar turai da ke da kaso mafi tsoka a tsarin tattalin arziki na Instex mai makon yin barazana mara dalili da alkawura kan takarda akwai, kamata ya yi su yi wani aikin jin kai mafi sauki, shi ne bada dama ga kamfanin harhada magunguna na Molnlycke ya sayarwa da Iran magungunan da take bukata, domin magance cutar fata ta ( EB) da ke addabar yara kanana.

Haka zalika ya bayyana cewa sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompoe ya yi Ikirarin cewa takunkumin Tattalin arziki na ta’adanci da Amurka ta sanyawa Iran ta tsara shi ne yadda za ta jefe alummar Iran cikin yunwa da kuma haramtawa mutanen da ba su san hawa ba balle sauka ba, samu magunguna da za su yi amfanin da su wajen warkar da Cutar fara ta EB dake addabar yara kanana.



/129