(ABNA24.com) Rundinar sojin Mali, ta sanar da mutuwar sojojin kasar biyu da kuma wasu bakwai da suka jikkata, biyo bayan da motarsu ta taka wani abun fashewa a tsakiyar kasar.
Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a lardin Diogani, dake jihar Mopti mai fama da matsalar tsaro a jiya Litini a kusa da iyaka da makobciyar kasar Burkina faso.
Kasashen Mali, Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar, dake a yankin Sahel, sun jima suna fama da matsalar tabarbarewar al’amuran tsaro masu nasaba da gungun kungiyoyin dake ikirari da sunan jihadi.
Lamarin dai na ci gaba da daukan hankalin kasashen duniya, duk da kasancewar sojojin Faransa dana MDD, da kuma na Afrika a yankin.
Baya hare haren da suka kaiwa nan da cen a yankin na Sahel, ‘yan tada kayar bayar na amfani da salon dasa nakiyoyi ko ababe masu fashewa wanda kuam ke sanadin mutuwar sojoji da dama.
Tun daga watan Nowamban da ya gabata, akalla sojojin Mali hudu ne, dana Burkina Faso biyu da kuma na Faransa guda suka gamu da ajalinsu a fashewar nakiya.
/129
4 Disamba 2019 - 04:23
Lambar labari: 991178
Rundinar sojin Mali, ta sanar da mutuwar sojojin kasar biyu da kuma wasu bakwai da suka jikkata, biyo bayan da motarsu ta taka wani abun fashewa a tsakiyar kasar.