4 Disamba 2019 - 04:21
​Zimbabwe : Mugabe Ya Baro Dalar Amurka Miliyan 10

Tsohon shugaban kasar Zimbabwe, mirigayi Robert Mugabe, ya baro kudade da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan goma a asusun ajiyar kudadensa na banki.

(ABNA24.com) Tsohon shugaban kasar Zimbabwe, mirigayi Robert Mugabe, ya baro kudade da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan goma a asusun ajiyar kudadensa na banki.

An kuma bayyana cewa tsohon shugaban, ya baro kaddarori na gidaje masu yawa a Harare babban birnin kasar, kamar yadda mujallar ‘’national The Herald, ta rawaito.

Saidai an bayyana cewa tsohon shugaban da ya rasu yana mai shakaru 95 a duniya, bai baro wasiyya ba.

Wannan ne ya sanya tilas a cikin makin makon nan mahukuntan kasar ta Zimbabwe suka nada wani wanda zai bi dindigin kaddarorin tsaohon shugaban kasar mai rasuwa.

A watan Oktoba day a gabata ne daya daga cikin ‘yayan mirigayi Mugabe din, mai suna Bona Chikowore, ta aike da wata wasika ga kotun kasar ta neman a gano mata kaddarorin da mahaifinta ya baro.

An dai kwashe shekaru a kssar ta Zimbabwe ana cece-kuce akan tarin dukiya da tsohon shugaban kasar da shi da iyalensa suka mallaka, wanda wasu ke zargin dukiyar day a wawushe ce a tsawan shekaru 37 yana mulkin kasar.




/129