24 Nuwamba 2019 - 05:03
Khatami:Amurka Da Faransa Da Jamus Sun Tabbatar Da hanunsu A Hargitsin Baya-Bayan Nan A Iran

Limamin da ya jagorancin sallar juma'a na birnin Tehran ya yi ishara kan tarzomar da ta wakana makon da ya gabata a nan kasar Iran, inda ya ce kasar Amurka ce ta dauki nauyin wannan tashin hankali kuma abin takainci kasashen Faransa da jamus sun tabbatar da hanunsu a wannan rikici.

(ABNA24.com) Limamin da ya jagorancin sallar juma'a na birnin Tehran ya yi ishara kan tarzomar da ta wakana makon da ya gabata a nan kasar Iran, inda ya ce kasar Amurka ce ta dauki nauyin wannan tashin hankali kuma abin takainci kasashen Faransa da jamus sun tabbatar da hanunsu a wannan rikici.

A makon da ya gabata ne, al'ummar kasar Iran suka gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin amincewarsu kan matakin da gwamnati ta dauka na kara farashin man fetir a nan birnin Tehran da wasu sauran biranan kasar, saidai wasu masu tayar da tarzoma wadanda suka samu horo daga kasashen ketare sun yi amfani da wannan dama wajen kone dukiyoyin mutane da na gwamnati, hatta da bankuna, motocin kwana-kwana da motoci sifiri ba su bari ba.

Ayat Sayyid Ahmad Khatami limamin da ya jagoranci sallar juma'a a nan birnin Tehran ya yi ishara kan tarzomar baya-bayan nan da ta wakana a nan kasar Iran, inda ya ce makiyan al'ummar Iran kimanin shekaru uku kenan suna gudanar da shirin tayar da tarzoma a nan kasar Iran indsa suka bayar da horo na musaman ga dakarunsu a ciki da wajen kasar, to amma al'ummar dake kishin kasarta ta samu nasarar dakile wannan makirci.

Yayin da yake ishara kan goyon bayan da wasu kasashen ketare ke bawa masu tayar da tarzomar, Ayat Khatami ya ce bayan gudumuwar kudi da gwamnatin Saudiya ke bawa wadannan mutane, ta basu damar yin amfani da kafofin sadarwarta domin ci da tayar da tarzoma a kasar ta Iran.

Har ila yau, Ayat Khatami ya ce kungiyoyin munafikai da suka kashe sama da mutane dubu 17 a kasar Iran na daga cikin wadanda suke goyon bayan wannan tarzoma.

Daga karshen Ayat Khatami ya yabawa al'ummar Iran da suka nuna kishin kasa, inda suka gudanar da jerin gwano na yin tir da masu tayar da tarzoma , kuma suka jadadda goyon bayansu ga tsarin musulinci, sannan ya gargadi gwamnati da ta yi aiki da alkawarin da ta dauka na hana hauhawar farashi na kayan masrufi a kasar.




/129