(ABNA24.com) Rahotanni daga Siriya na nuni da cewa mutane tara ne suka rasa rayukansu a wani harin bam da aka dana a mota a yankin Tal Abyad da sojojin Turkiyya suka mamaye a arewacin kasar.
Hukumar kare hakkin bil a adama ta OSDH, data rawaito labarin ta ce daga cikin mutanen da lamarin ya rusa dasu da akwai fararen hula hudu ciki har da yara biyu, sai kuma wasu mutum 22 da suka jikkata a harin.
Babu dai wata kungiya data dauki alhakin kai harin.
Yankin Tal-Abyad, na fuskantar hare hare ne tun bayan da Turkiyya ta kaddamar da farmakin soji kan kurdawan na Siriya a farkon watan da ya gabata.
Wannan dai ba shi na kero na farko ba da ake kai irin wannan hari a yankin na Tal-Abyad inda ko a kwanaki takwas da suka gabata akalla mutane 13 ne suka rasu a wani hari bam makamancin wannan, wanda kuma mahukunatn Turkiyya ke dangantawa dana mayakan kurdawa.
/129
24 Nuwamba 2019 - 04:55
Lambar labari: 988768
Rahotanni daga Siriya na nuni da cewa mutane tara ne suka rasa rayukansu a wani harin bam da aka dana a mota a yankin Tal Abyad da sojojin Turkiyya suka mamaye a arewacin kasar.