9 Nuwamba 2019 - 04:40
Iran : Rohani, Ya Jajantawa Wadanda Girgiza Kasa Ta Shafa

Shugaban kasar Iran, Dakta Hassan Rohani, ya aike da sakon ta’aziyya da jaje ga iyalan mutanen da girgizar kasar ta abka masu da cikin daren jiya.

(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran, Dakta Hassan Rohani, ya aike da sakon ta’aziyya da jaje ga iyalan mutanen da girgizar kasar ta abka masu da cikin daren jiya.

Mutane kimanin biyar ne aka rawaito cewa sun rasa rayukansu a girgizar kasar mai karfin maki 5,9 a ma’aunin girgizar kasa a yankin gabashin Azerbaijan dake arewa maso yammacin kasar ta Iran.

Ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu da akwai wasu mutane kimanin 300 da suka jikkata a cewar hukumomin yankin.

Masana harkokin girgiza kasa sun bayyana cewa kimanin mutane niliyan ashirin sun motsin girgizar kasar a Iran, kuma akwai yiyuwar a Turkiyya mai kakobtaka da kasar ma an ji motsin girgizar.

Girgizar kasa ba wai sabon abu ne ba a Iran, saidai kawai yanayin zuwan ta yakan bambanta lokaci zuwa lokaci, inda ake samun hassara rayukan mutane masu yawa, mafi muni ita ce ta shekara 2003, inda mutane sama da 26,000 suka rasa rayukansu.




/129